Bank verification number (BVN)

Shin wani zai iya amfani da BVN ya satar min kudi a Banki na?

Wannan ita ce tambayar da mutane da dama suke yawan yi a lokacin da kamfanoni ko ma’aikatu suka nemi mutum ya bayar da lambobin BVN din sa.

.

Kafin na bayar da wannan amsar, da farko dai ya kamata mu fara tambayar kanmu shin wai mene ne BVN?

BVN na nufin Bank Verification Number)

wato waɗansu lambobi da banki suke baiwa kowane mutum bayan sun karɓi waɗansu bayanai daga gare ka, wanda ya kun shi, cikakken sunanka, da adireshinka, da lambar wayarka da hoton fuskarka, da hotunan ‘yan yatsunka.

.

Wannan shine BVN kuma makasudin yin sa shine domin tabbatar da tsare dukiyar jama’a da tantance adadin jama’ar da suke yin mu’amala da bankuna a kowace kasa.

.

Bayan banki sun karɓi wannan bayanai duk wani asusun ajiyar kudi da zaka bude a kowane banki ba sai ka sake bayar da bayanan ka ba, kana basu wannan lambar shike nan suna da komai naka.

Sai mu koma ga amsar tambayar mu na cewar Shin ana iya satar kudin mutum ta amfani da BVN?

Wannan maganar kwata-kwata ba gaskiya bace, babu alaka da tsakanin BVN da Account number din ka ta wurin cire kudi.

Domin da za ka je banki cire kudi sai ka manta ka rubuta BVN dinka a takardar karbar kudi, mai biya ba zai iya sanin account dinka ba balle harya iya ciro maka kudin.

Akwai banbanci tsakanin BVN da PIN number dake jikin ATM dinka, wanda shi PIN din ATM shike da hatsari sosai wurin fadawa hannun miyagun mutane.

Dan haka babu wani mahaluki da zai ko iya ganin Account number ta BVN balle har ma Ya iya ganin asusunka Ya cire kudi,

Amma duk da haka ba mu ce ko ina ka saki BVN dinka ba.


YADDA ZAKA DUBA BVN NAKA

Ga yadda zaka duba bvn naka a layin da kayi register dasu kadanna *565*0# Daganan kudanna 1 reply zai kawo muku.

@BasiruLawan

Comments

Post a Comment

Popular Posts