BAYANI GAME DA ROOTING

BAYANI GAME DA ROOTING
Rooting a Hausance ko a sauwake ana nufin DAKE WAYA, ta yadda zaka samu dama akan injin wayar ka.
Idan kayi rooting wayar ka zaka samu cikakken iko akan wayar ka. Kowa yana da dalilin yin rooting amman zan dan kawo muku wasu muhimman dalilai da zai sa kayi rooting din wayar ka.
MUHIMMANCIN YIN ROOTING
1. Chanza sunan wayar ka.
2. Chanza version din wayar ka.
3. Cire ko wani irin application dake kan waya.
4. Shigar da duk application da ka ga dama akan wayar ka.
5. Wasu apps basu aiki sai a wayar da aka rooting din ta.
ILLOLIN ROOTING
Kaman yadda Rooting take da muhimmanci to tana da wasu illoli idan ka kayi.
1. Duk wayar da aka rootin din tana rushe tsarin yarjejeniyar wayar (Warranty)
2. Takan sa mastalar updating Firmware daga kamfanonin waya.
3. Saukin kamuwa da Virus.
4. Yakan sa wasu waya slow.
5. Wayar ka zata kasance babu cikakken tsaro.
INSHA ALLAHU ZAMU KAWO MUKU YADDA AKE ROOTING DA YADDA ZAKA UNROOT DIN WAYAR KA.
Muna maraba da masu tambaya, bada shawara ko Karin bayani akan rubutun mu.

Comments

Popular Posts