HANYA MAI SAUKI DA ZAKA YI BIDIYON SIRRI A WAYOYINKU NA ANDROID

HANYA MAI SAUKI DA ZAKA YI BIDIYON SIRRI A WAYOYINKU NA ANDROID
__________________________

Assalamu alaikum yan uwa masu bibiyar wannan page
Kamar dai yadda kuka gani a title na wannan post a yau insha Allah zan muku Karin bayani akan hanyar da zaka dauki bidiyon sirri a wayoyin ku na Android ta hanyar amfani da wani application.
Idan baza ku manta ba na taba yin posting a baya akan wannan application inda na Baku takaiccen bayanin yadda ake amfani dashi, hakan ne ma yasa wasu sukan tambaya game da Karin bayani, to a yau insha Allahu zan muku bayani dalla-dalla yadda kowa zai fahimci wannan application da kuma amfanin sa.
Hakika wannan application yana da matukar amfani, KAFIN na fara baku bayanin wannan application bari in Baku kadan daga cikin irin hanyoyin da idan kayi amfani da shi zai taimaka maka sosai.
1. zaka iya amfani da wannan application idan kana tunanin wani wanda kuke tare dashi zai yi zancen ka a bayan idon ka kamar dai yadda yanayin zamantakewar rayuwar mu ta yanzu ta sauya sai kaga mutum kuna zaune tare a gaban ka zai yabe ka sai ka bar wajan sai ka ya fara zagin ka ko ya fadi magana marar dadi akan ka, to idan har kana so kasan wane kallo mutum yake maka a bayan idon ka cikin sauki zaka iya amfani da wannan application
2. Idan kuma kana so kayi bidiyon a wuraren da baka so a gane kana bidyon to a nan ma wannan application zai taimaka ma sosai.
Kadan kenan daga cikin irin hanyoyin da wannan application zai taimaka ma.
SAI KU KARANTA YADDA application YAKE DA YADDA ZAKA YI AMFANI DA SHI
Da farko zaku dakko wannan application mai suna "irecorder" ku shiga wannan shudin rubutun na kasa domin dakko shi kai tsaye a wayoyin ku.
https://m.apkpure.com/irecorder-video-recorder/
com.i.video.recorder/download?from=details
Bayan kun dakko shi sai kuyi installing din shi sannan ku bude shi zaku ga ya nuno muku wata fuska mai dauke da alamar gurin yin recording kamar yadda kuka ga a hoton nan, da ga can sama kuma zaku ga a bangaren hagu akwai wani waje anyi layi-layi guda uku, a tsakiya kuma anyi alamar bidiyo can gefen dama kuma zaku ga alamar alarm
Dukkan wadannan wuraren zabuka ne na wannan application idan kana so ka fara gwada aikin application din kafin ka saita yanayin yadda kake so yana maka aiki kawai kai tsaye sai ka Danna wannan yar jar alamar video recording din nan Wanda ke tsakiya,
Idan kuma so kake ka saita lokacin da kake so ya fara aikin daukar bidiyo to sai ka shiga wajen da aka yi alamar alarm

Comments

Popular Posts