LABARI DA DUMI DUMINSA

Ɗaliban jami'a a Najeriya sun gurfana gaban kotu kan satar naira miliyan 9
EFCC
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC ta gurfanar da wani matashi mai yi wa ƙasa hidima da kuma ɗalibin Jami'ar Al-Hikmah bisa zargin satar kuɗi naira miliyan tara.
EFCC na tuhumar Nazim Usman Gomna, ɗan hidimar ƙasa wato NYSC a Jihar Jigawa, da Idris Shuaibu Suleiman, ɗalibin mataki na 4 a Jami'ar Al-Hikmah a Jihar Kwara.
Cikin ƙarar da ta shigar gaban Mai Shari'a Sikiru Oyinloye na Babbar Kotun Jihar Kwara, hukumar na zargin matasan biyu da haɗa baki wurin satar kuɗin makarantar da ɗalibai suka biya ta hanyar yin kutse a shafin intanet na jami'ar.
EFCC na tuhumarsu da aikata laifuka guda uku da suka haɗa da karkatar da kuɗin makaranta na ɗalibai da suka kai naira miliyan tara da dubu 100 zuwa asusunsu.
Da yake ɗage zaman shari'ar, alƙali ya bayar da belin mutanen kan kuɗi naira miliyan uku da rabi kowannensu tare da kawo mutum ɗaya da zai tsaya musu. Haka nan an ƙwace takardun tafiye-tafie nasu.

Comments

Popular Posts