SABUWAR SANARWA DAGA KAMFANIN WHATSAPP

SABUWAR SANARWA DAGA KAMFANIN WHATSAPP.
A satin nan kamfanin Whatsapp mallakin Facebook sanar da sababbin sauye sauye da yayi kuma ya umarci abokan huldar sa da su yarda da su kafin 8/2/2021 ko su daina amfani da manhajar ma'ana su share asusun su kwata-kwata.
"Dole ne ga duk mai amfani da manhajar ta whatsapp ya yarda da wadannan sharuda muddin zai ci gaba da amfani da ita". A cewar kamfanin. yaci gaba da cewa "wadannan sharuda zasu zama matakin tsare sirri da inganta aikace-aykace ga abokan mu'amalar mu"
Sharudan dai sun hadar da whatsapp zai ringa raba bayanai da Facebook sannan ga masu amfani da whatsapp domin harkokin kasuwanci dole suyi amfani da tsarin barbar kudi da bayarwa na Facebook. Domin karbar kudi ko bayarwa.
Ma'ana.
Idan kana amfani da whatsapp to duk bayanan ka da suka hadar da adreshin danbar ka. (IP. Adress) da bayanan wayar ka da duk datar ka kai tsaye whatsapp zai ringa aykewa dasu zuwa Facebooka za'a iya amfani dasu domin bin diddigin ka idan bukatar hakan ta taso amma ba yana nufin idan kayi wani abu za'a gani a Facebook ba.
Ga wadanda basu yarda da wannan sharuda ba zasu iya share asusun su kuma su daina amfani da whatsapp kwata-kwata.
Idan kuma basu yarda da sharudan ba kuma basu daina amfani da manhajar ba zuwa ranar. 8/Feb/2021. To kamfanin zai share asusun su amma zasu iya zuwa sashen taimako na whatsapp domin karbar bayanan su.

@basirucreativecenter.blogspot.com

Comments

Popular Posts