YADDA ZAKA KARKATAR DA KIRAN LIYI ZUWA WANI LAYIN AKAN KOWACE WAYA TA HANYAR AMFANI DA LAMBOBIN SIRRI

YADDA ZAKA KARKATAR DA KIRAN LIYI ZUWA WANI LAYIN AKAN KOWACE WAYA TA HANYAR AMFANI DA LAMBOBIN SIRRI Wani lokacin mutane da dama suna amfani da waya biyu ne domin ɗaya suna amfani da ita wajan kallon finafinai, hawa facebook, whatsapp, instagram, Youtube da dai sauran su. Ɗayar kuma suna amfani da ƙaramar wayar ne domin ƙira kawai. Ire iren wandanda ke amfani da waya biyu yawancin su suna barin wayar ne a gida ko kuma dai wani wuri na daban wato dai basu cika tafiya da babbar wayar ko ina ba saboda yanayin aiki. wasu sana tafiya da wayar ne badan suna son yawo da ita ba sai dan akwai layin da mutane suke kiran sa acikin wayar hakan tasa dole sai dai ka tafi da ita. To insha Allah ga musu irin wannan matsala kusa aranku daga yau matsalar ta ƙare. Har ila yau ta zamu nuna muku yadda zaka ɗaga kiran wayar da aka yiwa abokin ka ko matar ka ko wani dan uwan ka idan bai ɗaga ƙiran to ba kai tsaye sai kiran ya shigo wayar ka. Sanna kuma zamu nuna muku hanyar da idan aka kira wayar wani dan uwanka ko abokin ka idan wayar sa tana busy to sai ƙiran ya shigo cikin wayar ka kaitsaye. Nasan wasu zasu yi mamaki sosai wasu ma zasu yi tunanin ba gaskiya bane. To amma ga wanda ya sani wannan ba baƙon abu bane domin shekaru masu yawa ana amfani da wannan hanyar tun lokacin wayar tarho a inda zaka karkatar da kiran wayar tarho zuwa yawar tafi da gidan ka, kuma har gobe wannan hanya tana amfani akan wayoyin da muke amfani da su sai dai bakowane yasan wannan hanyar ba. Wannan hanya da turanci ana kiranta "call forward" ko "call divert" Ana saita call forward a wayoyin mu na hannu ta hanyar amfani da wasu lambobin sirri (ussd codes) GA YADDA ZAKU KARKATAR DA KIRAN DAGA LAYI ZUWA LAYI 1. Idan kana so ka karkatar da kiran waya zuwa wata wayar daban to ga yadda zaka yi > Dafarko sai ka ɗauki wayar da kake so ka karkatar da kiran layin ta zuwa layin wayar da ka zaɓa, ka tabbatar da kuɗin ƙira ko kaɗan ne a cikin layin wayar sai ka danna mata waɗannan lambobin kamar haka: **21*lambar wayar layin da ka zaɓa*10# Misali:- **21*08000000000*10# Sai ku danna ƙira. Bayan kun danna kira zai nuna muku yayi zaku ga wata 'yar kibiya a can saman screen ɗin wayar. To shiken yanzu kai tsaye idan an kira wayar zata tura kiran zuwa lambar layin da ka zaɓa Idan kuma ana so a cire tsarin akan wayar to sai a danna mata waɗannan lambobin kamar haka: ##21# sai a danna ƙira. 2. Idan kuma kana so idan an kira wayar ka tayi ringi baka ɗaga ba to ka kai tsaye ta kiran ya tafi zuwa wata wayar da ka zaɓa to sai to ga yadda zaka yi. > Dafarko zaka ɗauki wayar ka tabbata da kuɗin kira ko kaɗan ne acikin wayar. Sai ka danna mata waɗannan lambobin kamar haka: **61*lambar wayar da kake so kiran yana zuwa*10# sai ku danna ƙira zai nuna muku alamar yayi a can saman screen ɗin wayar. Daga yanzu duk wanda ya kira wannan wayar idan tayi ringi ba'a ɗaga ba to kai tsaye kiran zai tafi zuwa lambar layin wayar da ka zaɓa. Idan kuma ana so a cire tsarin to ga yadda zaku yi. Sai a danna waɗannan lambobin kamar haka: ##61# sai ku danna ƙira. 3. Idan kuma kana so ka kana ɗaga kiran layin da yake a jiye akan layin da yake kan wayar ka. To ga yadda zaku yi kawai ku dakko layin amma ku tabbata akwai kuɗin kira a cikin sa ko da ɗan kaɗan ne. Sai ku ɗaura layin akan waya sannan ku danna mata waɗannan lambobin kamar haka: **62*lambar layin da zaka na ɗaga ƙiran# Misali:- **62*08000000000# Sai ku danna ƙira. Zai nuna muku alamar yayi zaku ga alamar a can saman screen ɗin wayar. To sai ku sauke layin daga kan wayar. kawai duk lokacin da aka ƙira layin kai tsaye ƙiran zai tafi zuwa layin da ka zaɓa. Idan kuna so ku cire tsarin to sai ku maida layin akan wayar sannan ku danna waɗannan lambobin kamar haka: ##62# sai ku danna ƙira. Wannan ita ce hanyar da ake yin call forward ta hanyar amfani da lambobin sirri. 

Comments

Popular Posts