YADDA ZAKAI MONITORING WAYAR YARONKA KO KANINKA KO MATARKA KO WANI

YADDA ZAKA YI MONITORING WAYAR YARON KA KO KANIN KA.
A kullun Google suna cikin kokarin ganin sun kirkiri Applications masu amfani da ban sha'awa wadanda suka san lallai jama'a zasuji dadinsu, wannan Application din da zanyi maku bayani yanzu, Application ce da kamfanin Google suka kirkire ta saboda iyaye su kula da yadda yaransu suke gudanar da wayoyinsu na hannu da kula da tarbiyarsu, dan wannan dalilin ne suka kirkire ta ba dan wani dalili ba, karkayi amfani da ita wajen cutawa wani idan kayi haka, to kai da Allah kuma nima kaina bazan yafe maka ba.
Kamar yadda na fada maku a farko Akwai Application da yazo daga kamfanin Google me sana "Google Family Link" Kamfanin sunyi shine don ya taimaka wajen samun damar hada mahaifi da yaransa, Ta hanyar wannan Application zaka iya hade dukkan wasu da kakeso ka bibiya..
Application din na kyauta ne sannan yana bayyana komai gaskiya yanada da dadin aiki kuma yana da dadin sha'ani na tabbata duk wanda yayi ampani dashi zai burgeshi sosai matuka..
Amma applications din kala biyu ne akwai waanda zaka saka a wayarka a matsayin mahaifi sannan akwai wanda zaka saka a wayar da kakeson bibiya a matsayin wayar danka...
Naka a matsayin mahaifi shine; Google Family Link For Parent..
Na yaronka kuma Google Family Link for Kid. Ga hotunansu nan a kasa nasanya..
Idan katura wa yaron naka ko kuma wanda kakeso ka bibiya zaka iya boye Application din ta yadda bazai san akwai ta aciki ba..
Shi amfanin wadannan Application na asali anyi su ne kawai don su taimaka wajan mahaifi ko mahaifiya su kula da tarbiyar yayansu namiji ko mace misali wadannan Application zasu baka dama ka iya bibiyar duk inda danka yake ko kuma ina yaje ko daga ina yake ko ina zeje.
sannan akwai wanda su kuma zasu baka dama kana control din wayartasa ta yanda zaka iya kashe Internet din wayarsa sannan zaka iya kunnawa, hakan zaisa kana hana danka shiga Internet a lokacin karatu ko kuma a makaranta ko waje me amfani.
Akwai wanda su kuma zasu baka dama kana iya kashe wayar danka lokacin da kakeso sannan ka kunnata lokacin da kakeso ko kuma kasa screen ya dena aiki a kowanne lokaci ta yanda zaka samu damar sakashi bacci da wuri misali zaka iya cewa karfe 12 nayi na dare wayar tasa ta mutu saboda ya kwanta da wuri.
Sannan kuma Application din da aikin su shine su baka duk wani bayani akan wayar danka misali awa nawa yakeyi yana Game ko kuma tsawon awannin da yake batawa yana chatting sannan zata nuna maka dawa yake chat sannan me yake turawa..
Sannan akwai wanda suma zasu baka dama kana iya gano wannan kalar website danka yake shiga sannan in ya shiga me yakeyi sannan zaka iya hanashi shiga duk website din da baka so ya shiga a wannan yanayi cikin sauki...
To wadannan Application guda biyu a takaice amfanin su shine;
1. Misali abu na farko daga amfanin su shine sanin su zai sa ka iya kare kanka daga wanda yakeson cutar ka..
2. zaka iya amfani dasu wajan gane duk wanda kakeso ka bibiya uwa ko da ko miji ko mata ko ya da sauransu har ma'aikata a wajan aiki dukka ana iya bibiyar su.
3. zaka iya amfani da wadannan kalar Application don ka iya bibiyar wayarka saboda koda Allah yasa ta fadi ko kuma wani yayi kokarin saceta kai tsaye zaka iya ganinta cikin sauki sannan koda barawon yayi kokarin format din wayar bai isa yayiba...

Comments

Popular Posts