YANZU YANZU MASU KUTSE SUKA SACE NIN DIN YAN NIGERIA HAR MUTUM MILIYAN 3

 Yanzu-Yanzu: Masu kutse sun sace Lambobin NIN din 'yan Najeriya sama da Miliyan 3

Sama da mutane miliyan uku ne aka sace NIN dinsu, bayan da wani dan kutse da aka fi sani da Sam ya kutsa NIMC.

Dan kutsen ya yi alfahari da cewa ya samu damar shiga garken hukumar gwamnatin Najeriya kuma yana iya ci gaba da yin duk abin da ya ga dama tare da wasu muhimman bayanai da ke hannun sa.

Kutsen da aka yi wa hukumar NIMC ba wai kawai ya fallasa raunin tsaron yanar gizo na Najeriya ba ne, har ma ya nuna irin hadarin da mazauna kasar ke ciki a halin yanzu.

Harin na intanet da aki ya zo ne kasa da watanni biyu da Hukumar Sadarwa ta Najeriya a watan Nuwamban 2021 ta yi gargadin cewa wata kungiyar kutse ta Iran na shirin yin leken asiri ta intanet a fadin Afirka.

Sanarwar da hukumar ta fitar ta kuma bayyana cewa, masu satar bayanan na kai hare-hare a kan kamfanonin sadarwa, da masu samar da intanet, da ma'aikatun harkokin wajen Najeriya da wasu kasashen Afirka.

Har ila yau, lamarin ya zo ne watanni bayan da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, a lokacin da ta umarci ‘yan Najeriya da su yi rajistar lambar dan kasa, ta yi ikirarin cewa za ta dakatar da laifukan da ake aikatawa a kasar ciki har da wadanda ake tafkawa ta hanyar Intanet.

Da yake jawabi a yayin kaddamar da tsarin inganta harkokin ‘yan kasa a bangaren sadarwa na Najeriya da kuma sake fasalin manufofin kasa na yin rajistar katin SIM a watan Mayun 2021, Shugaba Buhari ya ce, “NIN zai rufe daya daga cikin raunin da ke tattare da tsarin tsaro. Za mu iya ganowa da sanin halayen ’yan Najeriya cikin sauĆ™i.

"Za mu gano mutane cikin sauki, gami da 'yan damfara."

Da yake tabbatar wa ‘yan Najeriya muhimmancin sabon tsarin, Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Digital, Isa Pantami, a watan Yunin 2021, ya yi ikirarin cewa al’amuran ta’addanci irinsu ‘yan fashi da garkuwa da mutane sun ragu matuka a cikin kasar sakamakon haka dagewar da gwamnati ta yi na mutane a Najeriya su yi rajistar NIN.

Pantami ya ci gaba da cewa, ingantaccen tsarin tattara bayanai zai kare ‘yan Najeriya fiye da kowane lokaci.

Pantami ya ci gaba da cewa, ingantaccen tsarin tattara bayanai zai kare ‘yan Najeriya fiye da kowane lokaci.

Sai dai duk da wannan tabbacin, sabon harin nan ya fallasa gazawar gwamnatin shugaba Buhari wajen kare 'yan Najeriya daga masu aikata laifuka ta yanar gizo.

Sama da ‘yan Najeriya miliyan 60 ne aka adana bayanan sirrinsu, a cewar hukumar NIMC.

Comments

Popular Posts