CIKAKKEN BAYANI AKAN PI NETWORK.

Daga Alƙalamin Muhammad Abdulrahman Sheka
"Amma fa rubutun ba na malalata a fagen karatu bane, yana da tsayi, amma cike yake da fawa'id countlesly!"
"Kafin ka fara karantawa, ina baka shawarar idan kana tunanin Pi zai fito ka siyar dashi a baka dollar. Toh wannan ne mafi girman kuskure na rayuwar ka"
⚠️⚠️⚠️⚠️⚠️ DISCLAIMER ⚠️⚠️⚠️⚠️⚠️
"MATUKAR KANA MINING DIN Pi Network KUMA KA KASA TSAYA KA KARANTA WANNAN RUBUTUN, TOH WALLAHI BAZAKA TABA FAHIMTAR ME KAKE MINING BA. KAI KO BAKA Pi Network WANNAN BINKICEN YANA DA MATUKAR MAHIMMANCI A MATSAYINKA NA DAN CRYPTO. IYA WANNAN BINKICEN KADAI YA ISHE KA GANE MENENE CRYPTOCURRENCY"
Bari dai nima dai yau na dan ce wani abu game da Pi Network, Wanda Zai Shafi Duk Wanda Ke mining na Pi a cikin wannan Gida. Bayan Bibiya ce dana dade inawa Pi tare da Nazari da Bincike Akan Shi, Magana ta domin allah ban samu kuskure ko daya a ciki ba a project din Pi. Duk abin da na iya gani a project din shine Mind Blowing Powerful Green Blockchain Project Cike da Alkawura da yawa Kamar: Freedom, Research, Vision, Displine, Technicalogy, Blockchain, Knowledge, Strategy, Time, Consistency, da Mafarkin Samar da Kudin bai daya.
Bari na fada maka wani abu. Wallahi babu cryptocurrencies a halin yanzu a kasuwa da yake da karfin iya wuce Bitcoin ko ya ƙalubalance shi idan da hali ma ya doke shi a kasuwa sai Pi. Na san za kuce sheka ya haulace don yin irin wannan sharhi, amma kafin ku jefe ni da banza kalma. ku ba ni dama in tabbatar da maganata. Zaɓin Pi Coin akan Bitcoin daidai yake da watsi da tsohon tsarin sufurin doki zuwa sabuwar hanyar sufuri a mota, jirgi dss.
Kafin na fara kare maganata wacce daidai take da asalin fahimtar menene Pi Network da ma cryptocurrency a takaice. Da farko zan so in fara tare da nunawa mana yadda abubuwa ke tafiya digitally a wannan zamanin da tsarin da ake son dora duniya na Netizens Society (Meterverse), a takaice kuma mu fadi yadda aka kawo Bitcoin duniya da matsalolin shi.
Idan ka kalli duniyar kasuwanci a zamaninmu. Mutum uku da suka fi kowa yin nasara a harkar kasuwanci na wannan karnin sune mutane ukun da suka karbi kasuwancin zamani na online. Akwai kimanin mutane Billion 7 a duniya. Amma manazarta sunce mutane biliyan 2 ne ke amfani da internet kuma fiye da haka suna shiga internet a kullum.
Netizens Society wadda yanzu ake son daukakawa zuwa (Metaverse World) duniya ce da ba ta da iyaka, a duniyarmu ta zahiri da kuma kasashe daban-daban da muke dasu akwai iyakoki, muna da gwamnatin tarayya da na jihohi da na ƙananan hukumomi na sannan kowace kasa tana da kudinta da ake kashewa a iyakar kasarta. Amma ka taya kayi nazari sosai zaka ga a duniyar mu ta online kamar (Facebook, Twitter, Instagram dss) duk babu wadanna sharudan. Kai tsaye zaka iya yiwa wanda yake kasar russia magana ta online ba tare da kasan ma a inda yake ba, zaka iyawa dan kasar india like ba tare da kayi visa da passport ba. Babu wani abu mai kama iyakokin border na kasa, jaha ko kananan hukumomi. Duniyar online duniya ce ta kyauta, cikakkiyar kyauta ma kuwa, wacce guri ne da dukan dangin ’yan Adam suke fuskantar asalin abinda ake kira yanci. Duk wannan abunda da kake gani na border, kudin takadda, yake-yake, talauci dss. Wasu tsirarun mutane ne yan jari hujja suke kirkira dan kansu. Kuma a yau muke kallon su a matsayin shuwagabanni da jagiorori.
Idan aka muka dubi wannan duniya ta Internet da ke da saurin bunkasuwa, akwai mutane da yawa wadanda sun dade suna tunanin kirkirar damarmaki da mutane zasu anfana ta yanar gizo tun da dadewa suka fara tunanin yadda za a samar da tsarin kasuwar duniyar online, suna son ya zama duniyar online ba kawai iya chating da posting din hauka za'a dinga yi ba, amma ya zamana akwai wata kasuwa da wadanda suke amfani da wannan duniyar suke cinikayya a ciki. Ka fadawa uban kowa wannan shine dalili na farko da yasa aka fara kirkirar fasahar blockchain.
Satoshi Nakamoto shi ne mutum ɗaya tilo, wanda ya sami nasara fiye da kowane mai hangen nesa da ya shiga cikin wannan gwagwarmayar kawowa duniyar online tsarin kashe kudi da kasuwanci, a yau kusan kowa dayake karanta rubutun nan ya fada cikin albarkar Sir Satoshi nakamoto na kirkirar tsarin Bitcoin na Blockchain.
Bitcoin a yau shine babban jagoran duk sauran cryptocurrencies a cikin kasuwancin harkar online ta yau. Lokacin da aka kirkiri Bitcoin akwai ka'idojin algorithms da dole ne ka bi kafin ka samu ka mallaki Bitcoin. Wannan shi ake kira (PoW= Proof of Work) shaidar aiki. Tsari ne na mining wanda daga ƙarshe yana baka kyautar BTC a wannan lokacin. Babu wani coin da ya taba isa ya gwada gwanji da BTC tun da duk wandannan coins din an ƙirƙira su ne suna bin tsarin Bitcoin.
Lokacin da aka kirkiri Bitcoin yawancin Netizens (Yan duniyar online) suna da babbar matsala a nan game da mining din Bitcoin, saboda yana da matukar wahala kuma yana cinye lokaci sosai, kuma yana da gurbata muhalli. Bayan gama garin mutane sun gama whalar mining din Bitcoin sai 'yan jari-hujja da suka san future na Bitcoin suka dinga siye shi daga hannun mutane suna boyewa, suna riƙe shi na dogon lokacin. Rashin iya yaduwar Bitcoin tsakanin Netizens (Yan Duniyar Online) hakan ya haifar da rashin daidaituwa a cikin al'ummar netizens, wanda, a zahirin gaskiya wannan ya sabawa asalin dalilin daya saka tun farko satoshi ya kirkiri Bitcoin, a yanzu halin da ake ciki gaba daya Bitcoin ya sauka daga asalin tsarin da yasa aka kirkire shi. Yan jari hujja wadanda a cypto muke kira da whales sun bata ma'anar Bitcoin.
Facebook Amazon da dai sauransu, a baya sun taba fito da wani shiri da suka kira da suna (libra Coin), duk da haka bai karbu ba, saboda abu ainihin niyya ga aikin. Kuma Netizens sun ƙi sayen wannan coins, saboda mutane ba wawaye ba ne, Ko da yaya waɗannan mugayen mutanen masu bushasshiyar zuciyar inji ( Mark Zuckerberg, elon musk dss) su kawo wa mutane abu to kansu suke son yiwa, idan kaga son kawo abu to tsantsar mugunta ce da son mamaye duniya. Hankali bai bawa mutane damar karɓar coin di libra ba.
Labarin da ke faruwa a yanzu shine waɗannan saitin miyagu masu zuciyar Mashin din da hankalin injina, waɗanda koyaushe so suke su dora mutane akan yadda za suyi tunani cikin tsarin imanin yadda suka dora mu, wanda mafi yawanci ke haddasa mumunan jari hujja dss. Yanzu suna son shigowa cikin intanet, suci gaba da kirkirarwa al'umma muguwar shaidaniyar dokar su na ƙirƙirar iyakoki, da saita matsayin mutane kamar; kamar first class citizens da second class na duniyar online wadda nan gaba zata koma Metaverse.
Misali yanzu a online kowa daidai yake da kowa, zan iya zuwa na gayawa duk wani mutum abinda nake so a lokacin da nake so sabanin a zahiri. Sun son dawo da duniyar online kamar yadda ake yi a duniyar gaske, wanda alhmdllh har yanzu sun kasa kama duniyar online da kuma Blockchain. Sai dai akwai buqatar son iyakance abubuwan da wayoyin hannu zasu dinga yi. Akwai burinsu na ganin duk abinda muke aikatawa a duniyar social media dss. Wanda kuma alhmdllh da zarar sun kawo wani tsari na mugunta sai kaga Allah yasa an kaucewa komai nasu. Toh fa anan maganar Pi Network tazo, fahimtar maganganun da nayi a baya ne kadai zai baka damar fahimtar menene asalin hikimar Pi Network, ina ga yau zaga fahimci cewa abinda da duk ka fahimta aka Pi a baya shirme ne. Pi ya wuce Bitcoin, yafi karfin tsarin Ethereum balantana sauran altcoin. Kai mafi girman kuskuren da kayi ma a baya shine tunanin cewa Pi Network coin ne, Toh abokina Pi yafi karfin a kirashi da coin.
Yanzu ga team na kwararru a fannin blockchain, idan nace team din kwararru ba ina nufin irin team na tokens da muke holding ba. A'a ina nufin wandanda suke da fahimtar yadda abubuwan rayuwa ke gudana, sun fito da mafita ga waɗannan matsalolin da ke fuskantar Blockchain, Duniyar Online da Bitcoin. Sun zo da tunanin juyin juya hali don canza duk tsarin aiki na kasuwar internet wanda shine Suka kira da Pi Network.
Sun sake tsara ka'idoji don ba wa masu amfani da yanar gizo wani kaso mai kyau na kasuwancin intanet ba kamar a crypto, don sake haɗa kan jama'a da kuma taimaka musu su fahimci haɗin gwiwar tattalin arzikin duniya, don katse mummunan da'irar magudin yan jari hujja, don haka kasuwa ce a cikinta akwai masu saye da yawa amma mai siyarwa ɗaya ne jal. Pi Network ko muce Pios wanda aka inganta akan tsarin Web3.0 yana so ya ba yan duniyar online daidaiton zamntakewar rayuwa, dimokiradiyya na gaskiya da 'yanci, suna so su karya duk wani amfani da kai na shugabannin gwamnati da duk rashin adalci. Cibiyar sadarwar Pi ta fi girma fiye da yadda kuke zato na rantse da Allah. Ina so in ƙarfafa ku da ku ci gaba da mining, Abokina Pi is more real than the unseen air you breath.
Pi Network yana so ya samar da sabuwar duniya da babu border, ba tare da centralization, it's absolutely free world, wawaye zai yi wuya a yi imani da da Pi, kuma shine ya sa suke da wauta da rashin hikima don gane damar da allah ke kawowa.
Bari inyi bayani mai sauki da kowa zai fahimta dukkan mun yarda cewa duk abin da ke faruwa na rayuwa yanzu an mayar dashi digital koh? Zan fara da kwatanta komai da music, bcos Na yi imani kowa yana son music. A farkon waƙar muna saurara me kawai lokacin da mawakin ke rairawa, sai mu haddace mu dinga rairawa mu ma, sai muka dawo kaset, daga nan munyi ƙaura daga shi zuwa CD ɗin, yanzu kuma MP3, a halin yanzu kuma an dawo harkar streaming babu buqatar ka aje akan wayarka.
To yanzu mu kawo shi a fannin harkar tattalin arziki, tun da farko muna da shanu da tumaki muna fatauci da su, ka bayar da akuya a baka gero dss, muka koma kan abinda ke daukar hankalin dan adam na zinare da azurfa, daga azurfa da zinari zuwa kudin takarda, mukan tashi daga kudin takarda zuwa credit card, muka kara tashi daga katin kiredit zuwa transaction na banki, muna tashi banki zuwa cryptocurrencies.🤣🤣🤣
Na aje maganata ta cewa Pi Network yafi Bitcoin, amma wannan a iya yanzu ne. Bamu san me zai faru gaba ba. Bitcoin yana da kyau amma yana da matsaloli da yawa da yake fuskanta, idan kayi karatun Blockchain zaka fahimci me nake magana akai.
Pi Network yana son kawo mafita ga waɗannan matsalolin da ke fuskantar fasahar Blockchain. Abubuwa da yawa fasahar Pi Network tana son kawo maganin su a harkar Blockchain. Saboda haka kada ka yaudari kanka kaci gaba kawai da mining, duk yadda kake tunanin Pi Network wallahi yafi, a shekarar da ta wuce ankashewa fasahar Pi Network kudi wanda yafi kudin da ake kashewa fasahar Blockchain na cryptocurrency gaba daya. Pi ba coin bane, balle token. Pi store of value Network ne da za'a kirkirar masa kasuwar sa ta kanshi. Amma fa magana ta domin allah ba nan kusa ba.
NA GAJI DA RUBUTU WALLAHI, AMMA AKAN Pi Network ZAN IYA KWANA INA BAYANI BAN GAMA BA. NAYI IMANI DA Pi FIYE DA CRYPTO, KUMA BAZAN DAINA MINING BA.
Bissalam......
Wallahu Ya'alamu....
Muhammad Abdulrahman Sheka.

Comments

Popular Posts